Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jewels

13 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da mutane suka ji wannan mugun magana, sai suka fara makoki. Ba kuma wanda ya sa kayan ado.

  2. Gama Ubangiji ya riga ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurinkai. In na yi tafiya da ku ko na ɗan lokaci, mai yiwuwa in hallaka ku. Yanzu sai ku tuɓe kayan adonku, zan kuwa yanke shawara a kan abin da zan yi da ku.’ ”

  3. Saboda haka Isra’ilawa suka tuttuɓe kayan adonsu a Dutsen Horeb.

  4. Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane, ’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”

  5. Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka daga gare su.

  6. Dukan zinariya da shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, waɗanda Musa da Eleyazar suka karɓa, suka kuma miƙa hadaya ga Ubangiji, nauyinta ta kai shekel 16,750.

  7. A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,

  8. ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu,

  9. kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu,

  10. da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu,

  11. Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki,

  12. na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki.

  13. Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.