Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jair

5 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Bayansa kuma sai Yayir daga Gileyad, wanda ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da biyu.

  2. Yana ’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir.

  3. Sa’ad da Yayir ya mutu, sai aka binne shi a Kamon.

  4. Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.

  5. (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.