Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Immortality: General references

119 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?

  2. In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,

  3. to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!

  4. Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada.

  5. Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’

  6. domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

  7. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

  8. Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,

  9. kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,

  10. da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.

  11. Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.

  12. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela

  13. Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.

  14. A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.

  15. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.

  16. Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.

  17. ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”

  18. Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.

  19. Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

  20. Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba.

  21. Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka.

  22. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci.

  23. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

  24. To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

  25. Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”