Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Feasts: Figurative

23 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Figurative

  1. Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa,

  2. “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.

  3. Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.

  4. “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’

  5. “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.

  6. Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.

  7. Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.

  8. “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.

  9. Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’

  10. Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.

  11. “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.

  12. Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

  13. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

  14. “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

  15. Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa.

  16. Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’

  17. “Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’

  18. “Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’

  19. “Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’

  20. “Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’

  21. “Bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’

  22. “Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’

  23. Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.”