Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Feast of Tabernacles

56 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.

  2. Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida.

  3. Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul.

  4. In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba.

  5. In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.

  6. Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.