- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Eunuch
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.”
Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan,
a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba.
Amma Ebed-Melek mutumin Kush, wani hafsa a fada, ya ji cewa sun sa Irmiya a rijiyar da ba ruwa. Yayinda sarki yana zama a Ƙofar Benyamin,
Ebed-Melek ya fita daga fadar ya ce masa,
“Ranka yă daɗe sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu a duk abin da suka yi wa Irmiya annabi. Sun jefa shi cikin rijiyar da ba ruwa, inda zai mutu da yunwa gama ba sauran wani burodi a birnin.”
Sai sarki ya umarce Ebed-Melek mutumin Kush, “Ka ɗauko mutane talatin daga nan ku fid da Irmiya annabi daga rijiyar kafin ya mutu.”
Saboda haka Ebed-Melek ya ɗauki mutane tare da shi suka shiga ɗaki a ƙarƙashin baitulmali a cikin fada. Ya ɗauko waɗansu tsofaffin tsummoki da tsofaffi riguna daga can ya kuma zurara su da igiya wa Irmiya a cikin rijiyar.
Ebed-Melek mutumin Kush ya ce wa Irmiya, “Ka sa waɗannan tsummoki da tsofaffin rigunan a hammatarka, ya zarga igiya.” Irmiya ya yi haka,
suka kuma ja shi sama da igiya suka fid da shi daga rijiyar. Irmiya kuwa ya zauna a sansanin matsara.
To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”
Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada,
a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan keken yaƙinsa yana karatun littafin annabin Ishaya.
Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin kekunan yaƙin nan ka yi kusa da ita.”