Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Crime

25 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kin rena abubuwana masu tsarki kika kuma ƙazantar da Asabbataina.

  2. A cikinki akwai mutane waɗanda suka nace su yi kisankai; a cikinki akwai waɗanda suke ci a dutsen tsafi suna yin ayyukan lalata.

  3. A cikinki akwai waɗanda suke kwana da matan mahaifansu; a cikinki akwai waɗanda suke kwana da mata a lokacin da suke al’adarsu, sa’ad da suke da rashin tsarki.

  4. A cikinki mutum guda yakan yi laifi abin ƙyama da matar maƙwabcinsa, wani cikin rashin kunya ya ƙazantar da matar ɗansa, wani kuma ya kwana da ’yar’uwansa, ’yar mahaifinsa.

  5. A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  6. Shugabanninki a cikinki suna kama da kyarketai masu yayyage ganimarsu; suna kisa suna kuma kashe mutane don samun ƙazamar riba.

  7. Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba.

  8. Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci.

  9. “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba.

  10. Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar.

  11. Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai.

  12. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,

  13. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.

  14. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne,

  15. da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu;

  16. su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi.

  17. Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

  18. “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”

  19. “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;

  20. hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,

  21. ba su kuma san hanyar salama ba.”

  22. “Babu tsoron Allah a idanunsu.”

  23. Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;

  24. bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,

  25. da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.