- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Covetousness
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma.
Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.
Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?
“Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, “Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, ɗan’uwana! Kaito, ’yar’uwata!’ Ba za su yi kuka dominsa ba, ‘Kaito, maigidana! Kaito, darajarsa!’
Za a binne shi kamar jaki za a ja shi a ƙasa a jefar a bayan ƙofofin Urushalima.”
A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
“ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.
Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya, yă jawo su waje da abin kamun kifinsa, yă tattara su cikin ragarsa, ta haka yakan yi murna da farin ciki.
Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.
ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu.
“Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’
Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.
Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
“Kaito ga wanda ya gina masarautarsa da ƙazamar riba don yă kafa sheƙarsa can bisa, don yă tsere wa zama kango!
“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.
Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.
Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.
“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”
“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?
Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’
Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.
Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.
Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama.