Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Covetousness: General references

97 ayoyi · 49 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’

  2. in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.

  3. Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.

  4. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.

  5. Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.

  6. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.

  7. Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

  8. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

  9. “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami. “Gaba ɗaya ba amfani! Kome ba shi da amfani!”

  10. Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar da yake fama a duniya?

  11. Zamanai sukan zo zamanai su wuce, amma duniya tana nan har abada.

  12. Rana takan fito rana ta kuma fāɗi, ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.

  13. Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa; tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.

  14. Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku, duk da haka teku ba ya cika. Daga inda rafuffukan suke fitowa, a can suke komawa kuma.

  15. Dukan abubuwa suna kawo gajiya, gaban magana. Ido ba ya gaji da gani, haka ma kunne yă ƙoshi da ji.

  16. Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.

  17. Kamar yadda kaya suke haɓaka, haka ma masu amfani da su. Kuma wane amfani ne suke ga mai shi in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?

  18. A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  19. “ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.

  20. Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya, yă jawo su waje da abin kamun kifinsa, yă tattara su cikin ragarsa, ta haka yakan yi murna da farin ciki.

  21. Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.

  22. ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu.

  23. “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’

  24. Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.

  25. Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.