Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Covetousness: Shall abound in the last days
Ayoyi game da Shall abound in the last days
Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.
Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya.
Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.