- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Constitution
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa.
Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali
don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.
Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima,
dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.
Maganar ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Sarki Zedekiya ya yi yarjejjeniya da duka mutane a Urushalima ya yi shelar ’yanci wa bayi.
Kowa ya ’yantar da bayinsa da suke Ibraniyawa, maza da mata; kada kowa ya riƙe bawa wanda yake mutumin Yahuda.
Saboda haka dukan fadawa da mutane suka yi yarjejjeniyar cewa za su ’yantar da bayinsu maza da mata ba za su kuwa ƙara riƙe su bayi ba. Suka yarda, suka kuma sake su.
Amma daga baya suka canja ra’ayoyinsu suka maido bayinsu suka kuma sāke bautar da su.
Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”
Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”
Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi.
Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”