Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Confessing Christ

25 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.

  2. An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.

  3. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.

  4. Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.

  5. Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege,

  6. gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

  7. Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’

  8. “’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.

  9. Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.

  10. Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba.

  11. Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.

  12. An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.

  13. Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,

  14. sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’

  15. “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”

  16. Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa, “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”

  17. Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu, “Masu mulki da dattawan mutane!

  18. In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi,

  19. to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.

  20. Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’

  21. Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”

  22. Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!

  23. Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.

  24. Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.

  25. Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”