Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cana

13 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,

  2. aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.

  3. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”

  4. Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”

  5. Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”

  6. Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.

  7. Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.

  8. Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka.

  9. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya

  10. ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”

  11. Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.

  12. Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum.

  13. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.