Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Caleb: Age of

4 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da Age of

  1. Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar,

  2. amma ’yan’uwana waɗanda muka je tare su suka ba da rahoton da ya sa zukatan mutane suka narke don tsoro. Ni kam na bi Ubangiji Allah da dukan zuciyata.

  3. Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da ’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’

  4. “Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar!