Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abib

8 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Wannan wata za tă zama a gare ku wata na farko, wata na fari na shekararku.

  2. “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar. “Kada wani yă zo a gabana hannu wofi.

  3. “Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.

  4. Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.

  5. A watan fari, dukan jama’ar Isra’ilawa suka iso Hamadan Zin. Suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta mutu, aka kuma bizne ta.

  6. Ku kiyaye watan Abib, ku kuma yi shagalin Bikin Ƙetarewar Ubangiji Allahnku, domin a watan Abib ne ya fitar da ku daga Masar da dad dare.

  7. A rana ta goma ga wata na farko, mutane suka haura daga Urdun suka sauka a Gilgal a gabashin iyakar Yeriko.

  8. Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma.