Skip to content

Zorah

9 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Zoreah

31.7600, 34.9600 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Zorah

  1. Biranen da suke a filayen kwari su ne, Eshtawol, Zora; Ashna,

  2. Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da, Zora, Eshtawol, Ir Shemesh,

  3. Akwai wani mutumin Zora, mai suna Manowa, daga kabilar Dan, matarsa kuwa bakararriya ce, ba ta haihuwa.

  4. Ruhun Ubangiji kuwa ya fara iza shi yayinda yake a Mahane Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.

  5. Sa’an nan ’yan’uwansa da dukan dangin mahaifinsa suka gangaro don su ɗauke shi. Suka kawo shi suka binne tsakanin Zora da Eshtawol a kabarin Manowa mahaifinsa. Ya yi mulkin Isra’ila shekara ashirin.

  6. Saboda haka mutanen Dan suka aika jarumawa guda biyar daga Zora da Eshtawol don su leƙi asirin ƙasar su kuma bincike ta. Waɗannan mutanen sun wakilci dukan kabilar. Suka ce musu, “Ku je, ku bincike ƙasar.” Mutanen suka shiga ƙasar tudu ta Efraim suka zo gidan Mika, inda suka kwana.

  7. Da suka komo Zora da Eshtawol, ’yan’uwansu suka tambaye su, “Me kuka gano?”

  8. Sai mutane ɗari shida daga kabilar Dan suka yi ɗamarar yaƙi, suka tashi daga Zora da Eshtawol.

  9. Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.