Tsallake zuwa abun ciki

Asaph

34 ayoyi · 5 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Asaph

Tace bisa littafi
  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.

  2. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Na Asaf. Zabura ce. Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni.

  3. Maskil na Asaf. Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina.

  4. Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.

  5. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka

  6. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

  7. Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

  8. Waƙa ce. Zabura ta Asaf. Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi.

  9. Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa.