Filibbiyawa 1:1-19
1
Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, Zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima.
2
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare ku.
3
Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.
4
A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum
5
saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu,
6
da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.
7
Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni.
8
Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.
9
Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa,
10
don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi,
11
cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.
12
To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara.
13
Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi.
14
Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro.
15
Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi.
16
Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara.
17
Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi.
18
Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki. I, zan kuwa ci gaba da farin ciki,
19
gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata.
Settings