Ƙidaya 32:1-13
1
Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki.
2
Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce,
3
“Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,
4
ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.”
5
Suka ce, “In mun sami tagomashi daga gare ka bari a ba da wannan ƙasa ga bayinka, tă zama mallakanmu. Kada ka sa mu haye Urdun.”
6
Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan?
7
Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
8
Haka iyayenku suka yi sa’ad da na aike su daga Kadesh Barneya don su dubo ƙasar.
9
Gama bayan suka haura Kwarin Eshkol suka hangi ƙasar, sai suka karya zuciyar Isra’ilawa daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
10
A ranar kuwa Ubangiji ya husata har ya yi wannan rantsuwa cewa,
11
‘Tabbatacce ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba, da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, domin ba su bi ni sosai ba,
12
ba ko ɗaya sai dai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze da Yoshuwa ɗan Nun, don su ne kaɗai suka bi Ubangiji da zuciya ɗaya.’
13
Ubangiji ya husata da Isra’ila har ya sa suka yi ta yawo a hamada shekara arba’in, sai da dukan tsaran da suka aikata wannan mugunta a gabansa, suka mutu.
Settings