Mattiyu 26:42-53
42
Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”
43
Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.
44
Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda.
45
Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi.
46
Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
47
Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su.
48
To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.”
49
Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.
50
Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.” Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.
51
Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.
52
Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu.
53
Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yă aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba?
Settings