Mattiyu 26:1-16
1
Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,
2
“Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”
3
Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,
4
suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.
5
Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”
6
Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,
7
wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.
8
Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!
9
Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”
10
Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.
11
Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.
12
Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata.
13
Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
14
Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci
15
ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.
16
Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
Settings