Skip to content
Mattiyu 12:6-30

Mattiyu 12:6-30

6
Ina faɗa muku cewa waniwanda ya fi haikali yana a nan.
7
Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’da ba ku zargi marar laifi ba.
8
Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
9
Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu,
10
a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”
11
Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?
12
Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”
13
Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
14
Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
15
Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
16
yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne.
17
Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,
18
“Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.
19
Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
20
Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
21
Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
22
Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
23
Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”
24
Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”
25
Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.
26
In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?
27
In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.
28
Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.
29
“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.
30
“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options