Skip to content
Yohanna 8:14-38

Yohanna 8:14-38

14
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, gama na san inda na fito da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ko inda za ni ba.
15
Kuna shari’a bisa ga ma’aunin mutane; ni kuwa ba na yin wa kowa shari’a.
16
Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni.
17
A cikin Dokarku a rubuce yake cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.
18
Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”
19
Suka tambaye shi suka ce, “Ina Uban nan naka?” Sai Yesu ya ce, “Ba ku san ni ko Ubana ba. Da kun san ni, da za ku san Ubana ma.”
20
Ya faɗi waɗannan kalmomi ne yayinda yake koyarwa a filin haikali, kusa da inda ake ajiye baye-baye. Duk da haka ba wanda ya kama shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
21
Har wa yau Yesu ya sāke ce musu, “Zan tafi, za ku kuwa neme ni, za ku kuma mutu cikin zunubinku. Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba.”
22
Wannan ya sa Yahudawa suka yi tambaya suka ce, “Zai kashe kansa ne? Shi ya sa yake cewa, ‘Inda za ni, ba za ku iya zuwa ba’?”
23
Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne.
24
Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”
25
Suka ce, “Wane ne kai?” Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne wannan da na sha faɗi muku.
26
Ina da abubuwa masu yawa da zan faɗa game ku in kuma yi muku shari’a. Amma wanda ya aiko ni mai aminci ne, abin da kuma na ji daga gare shi, shi nake gaya wa duniya.”
27
Ba su gane cewa yana yin musu magana game da Ubansa ba ne.
28
Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.
29
Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”
30
Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.
31
Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.
32
Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”
33
Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”
34
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.
35
Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.
36
Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske.
37
Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku.
38
Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options