Yohanna 1:19-34
19
To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne.
20
Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”
21
Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.”
22
A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”
23
Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”
24
To, waɗansu Farisiyawan da aka aika
25
suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”
26
Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.
27
Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
28
Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
29
Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
30
Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’
31
Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”
32
Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.
33
Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
34
Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
Settings