Ayuba 6:14-27
14
“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
15
Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani,
16
kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,
17
amma da rani sai yă bushe, lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.
18
Ayari sukan bar hanyarsu; sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.
19
Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.
20
Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai; sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.
21
Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako; kun ga abin bantsoro kuka tsorata.
22
Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina, ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,
23
ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina, ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?
24
“Ku koya mini, zan yi shiru; ku nuna mini inda ban yi daidai ba.
25
Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?
26
Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne, ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?
27
Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku.
Settings