Ayuba 40:15-24
15
“Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.
16
Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta.
17
Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.
18
Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.
19
Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.
20
Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa.
21
Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama.
22
Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
23
Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.
24
Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?
Settings