Skip to content
Ishaya 30:1-17

Ishaya 30:1-17

1
“Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi;
2
waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar.
3
Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya, inuwar Masar za tă jawo muku kunya.
4
Ko da yake suna da shugabanni a Zowan kuma jakadunsu sun iso Hanes,
5
kowa zai sha kunya saboda mutanen da ba su da amfani gare su, waɗanda ba sa taimako ko amfani, sai dai jawo kunya da da-na-sani.”
6
Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba,
7
zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne. Saboda haka na yi mata laƙabi Rahab Marar Yin Kome.
8
Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo, ka rubuta shi a kan littafi, cewa kwanaki suna zuwa zai zama madawwamin shaida.
9
Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.
10
Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.
11
Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”
12
Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu,
13
wannan zunubi zai zama muku kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa, da zai rushe nan da nan, ba tsammani.
14
Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu, ya ragargaje ƙaf har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga don ɗiba garwashin wuta ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”
15
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa, “Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.
16
Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’ Saboda haka za ku gudu! Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’ Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu!
17
Dubu za su gudu don barazanar mutum guda; da jin barazanar mutane biyar dukanku za ku yi ta gudu sai an bar ku kamar sandar tuta a kan dutse, kamar tuta a kan tudu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options