Skip to content
Ishaya 28:1-15

Ishaya 28:1-15

1
Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim, ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!
2
Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.
3
Za a tattaka wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.
4
Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa, da aka sa a kan kwari mai ba da amfani, zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari, da zarar wani ya gani ya kuma tsinka, zai haɗiye shi.
5
A wannan rana Ubangiji Maɗaukaki zai zama rawani mai daraja kyakkyawan rawani wa mutanensa da suka ragu.
6
Zai zama ruhun adalci gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a, wurin samun ƙarfi ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.
7
Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.
8
Duk amai ya rufe teburori kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.
9
“Wane ne yake so ya koyar? Ga wa yake bayyana saƙonsa? Ga yaran da aka yaye, ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne?
10
Gama haka yake. Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki a kan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan.”
11
To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani ba Allah zai yi magana da wannan mutane,
12
waɗanda zai ce, “Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”; da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa” amma sun ƙi su saurara.
13
Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama, Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi, mulki akan mulki, mulki a kan mulki; nan kaɗan, can kaɗan, domin su tafi su kuma fāɗi da baya, su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta.
14
Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’a ku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.
15
Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa, mun kuma yi yarjejjeniya da kabari. Sa’ad da zafi ya ratsa, ba zai taɓa mu ba, gama mun mai da ƙarya mafakarmu ruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options