Skip to content
Farawa 31:22-29

Farawa 31:22-29

22
A rana ta uku, sai aka faɗa wa Laban cewa Yaƙub ya gudu.
23
Sai Laban ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi bayan Yaƙub har kwana bakwai, ya kuma same shi a yankin tuddan Gileyad.
24
Sai Allah ya bayyana ga Laban mutumin Aram a mafarki da dare, ya ce masa, “Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu, ko mai kyau ko marar kyau.”
25
Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma.
26
Sai Laban ya ce wa Yaƙub, “Me ke nan ka yi? Ka ruɗe ni, ka kuma ɗauki ’ya’yana mata kamar kamammun yaƙi.
27
Me ya sa ka gudu a ɓoye ka kuma ruɗe ni? Me ya sa ba ka faɗa mini don in sallame ka da farin ciki da waƙoƙi haɗe da kiɗin ganguna da garayu ba?
28
Ba ka ma bari in sumbaci jikokina da ’ya’yana mata in yi musu bankwana ba. Ka yi wauta.
29
Ina da iko in cuce ka; amma jiya da dare Allahn mahaifinka ya faɗa mini, ‘Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu ko mai kyau ko marar kyau.’
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options