Farawa 31:1-16
1
Yaƙub ya ji cewa ’ya’ya Laban mazan suna cewa, “Yaƙub ya kwashe dukan abin da mahaifinmu yake da shi, ya kuma sami dukan wannan arziki daga abin da yake na mahaifinmu.”
2
Yaƙub kuma ya lura cewa halin Laban gare shi ya canja ba kamar yadda yake a dā ba.
3
Sai Ubangiji ya ce wa Yaƙub, “Koma ƙasar kakanninka da kuma danginka, zan kuwa kasance tare da kai.”
4
Saboda haka Yaƙub ya aika a ce wa Rahila da Liyatu su zo jeji inda garkunan suke.
5
Sai ya ce musu, “Na ga cewa halin mahaifinku gare ni ba kamar yadda dā yake ba, amma Allah na mahaifina yana tare da ni.
6
Kun san cewa na yi aiki wa mahaifinku da dukan ƙarfina,
7
duk da haka mahaifinku ya cuce ni ta wurin sauya albashina sau goma. Amma dai, Allah bai yardar masa yă yi mini lahani ba.
8
In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne.
9
Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni.
10
“A lokacin ɗaukar cikin garken, na taɓa yin mafarki inda na ga bunsuran da suke barbara da garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne.
11
Sai mala’ikan Allah ya ce mini a mafarkin, ‘Yaƙub.’ Sai na amsa na ce, ‘Ga ni.’
12
Ya ce, ‘Ɗaga idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan garken, masu dabbare-dabbare, ko babare-babare, ko masu zāne-zāne ne, gama na ga dukan abin da Laban yake yin maka.
13
Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’ ”
14
Sai Rahila da Liyatu suka amsa suka ce, “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne?
15
Ba kamar baƙi ne yake ɗaukarmu ba? Ba sayar da mu kaɗai ya yi ba, har ma ya yi amfani da abin da aka biya saboda mu.
16
Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da ’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.”
Settings