Fitowa 18:1-12
1
Ana nan sai Yetro firist na Midiyan, kuma surukin Musa, ya ji duk abin da Allah ya yi wa Musa da mutanensa Isra’ila, da kuma yadda Ubangiji ya fitar da Isra’ila daga Masar.
2
Bayan da Musa ya tura matarsa Ziffora gida, sai surukinsa Yetro ya karɓe ta
3
da ’ya’yanta biyu maza. Ana kira ɗaya Gershom, domin Musa ya ce, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa”;
4
ɗayan kuma Eliyezer, domin ya ce, “Allah mahaifina ya taimake ni ya cece ni daga takobin Fir’auna.”
5
Yetro surukin Musa tare da ’ya’yan Musa da matarsa suka zo wurin Musa a hamada, inda suka kafa sansani kusa da dutsen Allah
6
Yetro ya riga ya aika wa Musa cewa, “Ni surukinka Yetro, ina zuwa wurinka tare da matarka da ’ya’yanka maza biyu.”
7
Sai Musa ya tafi yă taryi surukinsa, ya sunkuya ya yi masa sumba. Suka gai da juna, sa’an nan suka shiga tenti.
8
Musa kuwa ya faɗa wa surukinsa duk abubuwan da Ubangiji ya yi wa Fir’auna da Masarawa domin Isra’ila, da batun wahalolin da suka sha a hanya, da yadda Ubangiji ya cece su.
9
Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa.
10
“Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa.
11
Yanzu na san cewa Ubangiji ya fi kowane allah, gama ya yi wannan ga masu girman kai da kuma waɗanda suka wulaƙanta Isra’ila.”
12
Sa’an nan Yetro surukin Musa, ya kawo hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu wa Allah, Haruna ya zo tare da dukan dattawan Isra’ila, suka ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.
Settings