Skip to content
Daniyel 6:10-23

Daniyel 6:10-23

10
To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.
11
Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi.
12
Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”
13
Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”
14
Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi.
15
Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”
16
Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!”
17
Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel.
18
Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.
19
Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki.
20
Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?”
21
Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe!
22
Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.”
23
Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options