Daniyel 6:10-15
10
To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.
11
Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi.
12
Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”
13
Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.”
14
Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi.
15
Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”
Settings