Tsallake zuwa abun ciki
1 Tessalonikawa 5:12-27

1 Tessalonikawa 5:12-27

12
To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.
13
Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.
14
Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
15
Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
16
Ku riƙa farin ciki kullum;
17
ku ci gaba da yin addu’a;
18
ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
19
Kada ku danne aikin Ruhu.
20
Kada ku rena annabci,
21
amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,
22
ku ƙi kowace mugunta.
23
Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
24
Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
25
’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.
26
Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki.
27
Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options