Skip to content
1 Tessalonikawa 5:1-11

1 Tessalonikawa 5:1-11

1
To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
2
gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
3
Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
4
Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
5
Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
6
Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
7
Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
8
Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
9
Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
10
Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
11
Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options