Skip to content
1 Sama’ila 26:1-9

1 Sama’ila 26:1-9

1
Zifawa suka je wurin Shawulu a Gibeya suka ce, “Ashe, ba Dawuda ne ya ɓuya a tudun Hakila da yake fuskantar Yeshimon ba?”
2
Sai Shawulu ya tashi ya gangara zuwa Jejin Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra’ila. Suka fita neman Dawuda a can.
3
Shawulu ya yi sansani a bakin hanyar zuwa tudun Hakila mai fuskantar Yeshimon. Amma Dawuda yana zaune a jeji. Sa’ad da ya ga Shawulu ya biyo shi har zuwa can,
4
sai ya aiki ’yan leƙen asiri su tabbata lalle Shawulu ya iso can.
5
Sai Dawuda ya kintsa ya tafi inda Shawulu ya yi sansani. Ya ga inda Shawulu da Abner ɗan Ner shugaban ƙungiyar soja suka kwanta. Shawulu yana kwance a cikin sansani tare da sojoji kewaye da shi.
6
Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”
7
Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.
8
Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”
9
Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira?
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options