Skip to content
1 Sama’ila 26:13-20

1 Sama’ila 26:13-20

13
Sa’an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefen kwarin, ya hau kan wani tudu mai ɗan nisa inda Shawulu tare da mutanensa suke. Akwai babban fili tsakaninsu.
14
Sai Dawuda ya kira sojojin Shawulu da kuma Abner ɗan Ner ya ce, “Abner ba za ka amsa mini ba?” Abner ya ce, “Wane ne yake kira yana damun sarki haka?”
15
Dawuda ya ce wa Abner, “Wane irin mutum ne kai? Ba kai ne soja mafi iya yaƙi a Isra’ila ba? Don me ba ka yi gadin ranka yă daɗe, sarki da kyau ba? Ɗazu wani ya shiga tsakiyarku don yă kashe ranka yă daɗe, sarki.
16
Abin da ka yi bai yi kyau ba. Muddin Ubangiji yana a raye kai da mutanenka kun cancanci mutuwa, domin ba ku lura da maigidanku shafaffe na Ubangiji ba. Ka duba kewaye da kai, ina māshi da kuma butar ruwan da suke kusa da kansa?”
17
Shawulu ya gane muryar Dawuda, sai ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Dawuda ya ce, “I, muryata ce ya ranka yă daɗe, sarki.”
18
Ya ƙara da cewa, “Don me ranka yă daɗe, yake fafarata? Mene ne na yi? Wane abu ne aka same ni da laifi a kai?
19
To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’
20
Kada ka yarda jinina yă zuba a ƙasa nesa da gaban Ubangiji. Sarkin Isra’ila ya fito yă nemi kuɗin cizo kamar mai farautar kazan duwatsu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options