1 Sama’ila 26:21-25
21
Sai Shawulu ya ce, “Na yi zunubi ka dawo Dawuda ɗana. Ba zan yi maka kome ba, domin ka darajarta raina yau. Lalle na yi wawanci! Na yi babban kuskure.”
22
Dawuda ya ce, “Ga māshin sarki, ka aiko wani saurayi yă zo yă karɓa.
23
Ubangiji yakan sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma ba zan sa hannuna a kan shafaffe na Ubangiji ba.
24
Kamar yadda na ga darajar ranka yau. Haka ma bari Ubangiji yă ga darajar raina, yă cece ni daga dukan wahala.”
25
Sai Shawulu ya ce wa Dawuda, “Allah yă albarkace ka ɗana, Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, tabbatacce kuma ka yi nasara.” Sai Dawuda ya yi tafiyarsa, Shawulu kuwa ya koma gida.
Settings