Skip to content
1 Sama’ila 26:5-12

1 Sama’ila 26:5-12

5
Sai Dawuda ya kintsa ya tafi inda Shawulu ya yi sansani. Ya ga inda Shawulu da Abner ɗan Ner shugaban ƙungiyar soja suka kwanta. Shawulu yana kwance a cikin sansani tare da sojoji kewaye da shi.
6
Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”
7
Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.
8
Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”
9
Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira?
10
Muddin Ubangiji yana a raye, Ubangiji da kansa zai buge shi, ko yă mutu a lokacinsa, ko kuma yă mutu a wurin yaƙi.
11
Amma Allah yă sawwaƙa in sa hannu a shafaffen Ubangiji, ka ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da kansa mu tafi.”
12
Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options