1 Korintiyawa 1:1-17
1
Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,
2
Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu.
3
Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
4
Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu.
5
Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku
6
gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku.
7
Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
8
Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
9
Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.
10
Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.
11
’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku.
12
Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”
13
Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne?
14
Ina godiya domin ban yi wa wani baftisma a cikinku ba, sai dai Kirisbus da Gayus kaɗai.
15
Don haka, ba wanda na iya cewa an yi muku baftisma a cikin sunana.
16
(I, na kuma yi wa iyalin gidan Istifanas baftisma, ban da wannan, ban tuna da wani da na yi masa baftisma ba.)
17
Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa.
Settings