Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Witness of the Holy Spirit: Borne against all unbelievers
Ayoyi game da Borne against all unbelievers
Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu.
Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa,
“ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”
Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’