Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Voice

12 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’ad da halittun suke tafiya, sai na ji ƙarar fikafikansu, kamar rurin ruwaye masu gudu, kamar muryar Maɗaukaki, kamar hayaniyar rundunar mayaƙa. In sun tsaya cik, sukan sauko da fikafikansu.

  2. Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi. Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.

  3. Sai aka ji ƙarar fikafikan kerubobin har a filin waje, kamar muryar Allah Maɗaukaki sa’ad da ya yi magana.

  4. Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba,

  5. Uba, ka ɗaukaka sunanka!” Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.”

  6. Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce mala’ika ne ya yi masa magana.

  7. Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba.

  8. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

  9. Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

  10. Mutanen da suke tafiya tare da Shawulu suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba.

  11. Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’

  12. “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.