Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Virgin: Character of, to be protected

7 ayoyi · 10 fannoni

Ayoyi game da Character of, to be protected

  1. Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata.” Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,

  2. dattawan kuwa za su ɗauki mutumin su hukunta shi.

  3. Za su ci masa tara shekel azurfa ɗari, su ba mahaifin yarinyar, domin wannan mutum ya ba wa budurwa mutuniyar Isra’ila mummunan suna. Za tă ci gaba da zama matarsa; ba kuwa zai sake ta ba muddin ransa.

  4. Amma fa in zarge gaskiya ne, ba a kuwa sami shaidar budurcin yarinyar ba,

  5. sai a kawo ta a ƙofar gidan mahaifinta, a can mazan gari za su jajjefe ta da dutse har tă mutu. Ta yi abin kunya a Isra’ila ta wurin lalaci a yayinda take a gidan mahaifinta. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  6. In mutum ya sadu da budurwa a gari wadda aka yi alkawarin aure, ya kuma kwana da ita

  7. sai ku ɗauki su biyu zuwa ƙofar wannan gari, ku jajjefe su da dutse har su mutum, za a kashe yarinyar domin tana a cikin gari ba ta kuwa yi ihu neman taimako ba, za a kashe mutumin domin ya yi lalata da matar wani. Dole ku fi da mugu daga cikinku.