Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Under the Law Atonement

34 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.

  2. A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon.

  3. Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.

  4. Kashegari Musa ya ce wa mutane, “Kun yi zunubi mai girma. Amma yanzu zan hau wurin Ubangiji; wataƙila zan iya yin kafara domin zunubinku.”

  5. Don haka Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Kaito, mutanen nan sun yi zunubi mai girma! Sun yi wa kansu allolin zinariya.

  6. Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.”

  7. Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina.

  8. Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.”

  9. yă kuma yi da wannan bijimi kamar yadda ya yi da bijimi na hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominsu, za a kuwa gafarta musu.

  10. Sa’an nan zai ɗauki bijimin waje da sansani yă ƙone shi kamar yadda ya ƙone bijimi na fari. Wannan ita ce hadaya don zunubi domin jama’a.

  11. “ ‘Sa’ad da shugaba ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji Allahnsa ya umarta, to, ya yi laifi.

  12. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo bunsuru marar lahani a matsayin hadayarsa.

  13. Zai ɗibiya hannunsa a kan bunsurun yă kuma yanka shi a inda ake yankan hadayar ƙonawa a gaban Ubangiji. Hadaya ce ta zunubi.

  14. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.

  15. Zai ƙone dukan kitse a kan bagade kamar yadda ya ƙone kitsen hadaya ta salama. Ta haka firist zai yi kafara saboda zunubin mutumin, za a kuwa gafarta masa.

  16. “ ‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.

  17. Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi.

  18. Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.

  19. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.

  20. Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.

  21. “ ‘Idan kuwa daga cikin ’yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo ’yar tunkiya marar lahani.

  22. Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta hadaya don zunubi a inda ake yankan hadayar ƙonawa.

  23. Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubin da yatsarsa yă zuba a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.

  24. Zai kuma ɗebe kitsenta duka kamar yadda a kan ɗebe na ragon hadaya ta salama. Firist zai ƙone shi a bisa bagaden a bisa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ta haka firist ɗin zai yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.

  25. Ubangiji ya ce wa Musa,