Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Trespass Offering: Cleansing of a leper

6 ayoyi · 25 fannoni

Ayoyi game da Cleansing of a leper

  1. “Waɗannan su ne ƙa’idodi domin mutumin da yake da cuta a lokacin tsabtaccewarsa, sa’ad da aka kawo shi ga firist.

  2. “Sa’ad da firist zai ɗauki ɗaya daga cikin ragunan ya kuma miƙa shi kamar hadaya don laifi, tare da moɗan mai; zai kaɗa su a gaban Ubangiji kamar hadaya kaɗawa.

  3. Zai yanka ɗan ragon a tsattsarkan wuri inda ake yanka hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa. Gama yadda hadaya ta zunubi ta firist ne, haka hadaya domin laifi ma, hadaya ce mafi tsarki.

  4. Firist ɗin zai ɗiba jinin hadaya don laifin ya zuba a leɓatun kunnen dama na wanda za a tsabtacce, a babbar yatsar hannunsa na dama a kuma a babbar yatsar ƙafa damansa.

  5. “In kuwa mutumin matalauci ne ba zai iya samu waɗannan ba, to, dole yă ɗauki ɗan rago guda kamar hadaya don laifi a kaɗa don a yi kafara dominsa, tare da humushin garwa gari mai laushi haɗe da mai don hadaya ta gari, da moɗa na mai,

  6. da kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, wanda zai iya samu, ɗaya domin hadaya don zunubi ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa.