Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Transfiguration

36 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.

  2. Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi.

  3. Amma Musa ya kira su, sai Haruna da dukan shugabannin jama’ar suka zo wurinsa, ya kuwa yi musu magana.

  4. Daga baya sai dukan Isra’ilawa suka zo kusa da shi, ya kuma ba su dukan dokokin da Ubangiji ya ba shi a Dutsen Sinai.

  5. Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa.

  6. Amma duk sa’ad da ya je gaban Ubangiji don yă yi magana da shi, sai yă tuɓe lulluɓin har sai ya fito. Kuma duk sa’ad da ya fito yă faɗa wa Isra’ilawa abin da aka umarce shi,

  7. sai su ga fuskarsa tana ƙyalli. Sa’an nan Musa yă sāke lulluɓe fuskarsa, har sai ya shiga don yă yi magana da Ubangiji.

  8. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.

  9. Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  10. Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

  11. Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

  12. Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice.

  13. Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”

  14. Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

  15. Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”

  16. Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.

  17. Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su.

  18. Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  19. Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

  20. (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)

  21. Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”

  22. Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.

  23. Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.

  24. Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”

  25. Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya.