Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titus

57 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.

  2. Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah

  3. duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,

  4. da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu,

  5. Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.

  6. Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka.

  7. Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can.