Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titus: Paul's love for

7 ayoyi · 11 fannoni

Ayoyi game da Paul's love for

  1. duk da haka, ban sami salama a zuciyata ba domin ban sami ɗan’uwana Titus a can ba. Sai na yi bankwana da su na wuce zuwa Makidoniya.

  2. Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus,

  3. ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.

  4. Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa. Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka.

  5. Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya.

  6. Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne.

  7. Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya. Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.