Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Owl: Inhabits deserted cities and houses

6 ayoyi · 7 fannoni

Ayoyi game da Inhabits deserted cities and houses

  1. Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.

  2. Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta; babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can. Allah zai miƙe a kan Edom magwajin bala’i da ma’aunin kango.

  3. Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba, dukan sarakunanta za su ɓace.

  4. Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi.

  5. Halittun hamada za su sadu da kuraye, awakin jeji za su yi ta kiran juna; a can halittun dare su ma za su huta su kuma nemi wurin hutu wa kansu.

  6. “Saboda haka halittun hamada da kuraye za su zauna a can, a can kuma mujiya za tă zauna. Ba za a ƙara zauna ko a yi zama a cikinta ba daga tsara zuwa tsara.