Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shekinah

10 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.

  2. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna, kada yă riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada yă mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.

  3. Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da SunanUbangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin.

  4. Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji.

  5. Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.

  6. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka

  7. “Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya.

  8. To, fa, ɗaukakar Allah na Isra’ila ta haura daga bisa kerubobi, inda ta kasance, ta tashi zuwa bakin madogarar ƙofar haikali. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da lilin wanda ya rataye jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa

  9. Sai ɗaukakar Ubangiji ya tashi daga bisa madogarar ƙofar haikali ya kuma tsaya a bisa kerubobi.

  10. A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.